Hukumar tsaro ta farin kaya DSS, ta gargaɗi ‘yan Nijeriya su yi taka tsan-tsan a lokutan bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara, domin akwai yiwuwar samun hare-haren ‘yan ta’adda.
Hakan ya na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun ta Peter Afunanya.
Sanarwar ta ce, Hukumar DSS na son sanar da jama’a game da wasu shirye-shiryen miyagu na kai hare-hare a muhimman wuraren taruwar jama’a a lokutan bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.
Afunanya, ya ce hare-haren da ake tsammanin za su faru, wani shiri ne na miyagu domin yi wa gwamnatin tarayya zagon-ƙasa.