Home Labaru Yawan Mutanen Da Suka Kamu Da Cutar Korona A Najeriya Ya Kai...

Yawan Mutanen Da Suka Kamu Da Cutar Korona A Najeriya Ya Kai 221,071

163
0

Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum dubu 1 da 51 ne suka kamu da cutar korona a faɗin Najeriya ranar Alhamis.

NCDC ta ce daga cikin sabbin wadanda suka kamu jihar Lagos tana kan gaba da mutane 595 sai babban birnin tarayyar Abuja na da mutum 238, jihar Rivers tana da mutum 79 yayin da Oyo ke da mutum 51.

Sai Ondo tana da mutum 32, Jihar Flato na da mutum 20, Akwa Ibom tana da mutum 11, Ogun tana da mutum 7, yayin da Bayelsa da Kano na da mutum 5 kowanen su, Jihar Kwara kuma tana da mutum 4

Yanzu dai adadin waɗanda suka kamu da cutar a Najeriya tun bayan ɓullarta ya kai dubu 221 da 071 amma kuma an sallami dubu 211 da 345 daga asibiti.

Yawan waɗanda suka rasa rayukan su sanadin cutar kuwa ya kai mutum dubu 2 da 983.

Leave a Reply