Home Labaru Sojin Najeriya Sun Yi Nasarar Kakkabe Magoya Bayan Bello Turji A Sokoto

Sojin Najeriya Sun Yi Nasarar Kakkabe Magoya Bayan Bello Turji A Sokoto

89
0

‘Yan bindiga da dama ne daga cikin ‘yan kungiyar Bello Turji  a Jihar Sokoto aka bayyana cewar sun mutu sakamakon bude wutar da soji suka yi musu a kauyen Katanga dake karamar hukumar Isa.

Shaidun gani da ido sun ce babban kwamandan sojin dake kula da runduna ta 8 Manjo Janar Uwem Bassey ya jagoranci tawagar sojoji tare da manyan jami’an sa a cikin motocin yaki sama da 20, wadanda suka yiwa ‘Yan bindigar kofar rago, yayin da sojin sama suka taimaka musu da ruwan wuta ta sama.

Bayanan dake zuwa daga ‘Yankin sun ce sojojin sun yi nasarar kashe ‘Yan bindigar da dama tare da kona matsugunin su, yayin da suka ci gaba da bin sawun wadanda suka tsere daga kauyen domin kaucewa ruwan wutar.

Janar Bassey ya sha alwashin murkushe wadannan ‘Yan ta’addan da suka hana zaman lafiya a yankin tunda ya karbi ragamar jagorancin rundunar samar da zaman lafiya ta ‘Operation Safe Haven’, kuma rahotanni sun tabbatar da cewar da kan sa yake jagorancin sojojin dake kai harin cikin dazukan jihar.