Home Labaru An Bankado Almundahanar N8.5Bn A Majalisar Dokoki Ta Kasa

An Bankado Almundahanar N8.5Bn A Majalisar Dokoki Ta Kasa

88
0

Ofishin Mai Binciken Kudi na Tarayya ya gano badakalar sama da Naira biliyan 8  a zaurukan Majalisun dokoki na Tarayya.

Rahoton binciken kudin ya gano yadda shugabancin zaurukan biyu suka kashe Naira biliyan uku a Majalisar Dattawa da wasu biliyan 5.5 a a Majalisar Wakilai a shekarar 2019 ba tare da shaidar kashe kudaden ba.

Mai Binciken Kudi na Tarayya, Aghughu Adolphus, a rahoton, ya bankado yadda Majalisar Dattawa, da Majalisar Wakilai da Hukumar Kula da Harkokin Majalisun Dokoki Ta Kasa suka kashe kudaden ba bisa ka’ida ba.

Rahoton da ya gabatar wa Akawun Majalisar a watan Agusta ya ce  an kashe kudaden ne a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2018 ba tare da cike takardun da suka dace ko rasidin kayan da aka saya ba.

A shekarar da ta gabata ne Kwamitin Kudaden Gwamnati na Majalisar ya kaddamar da bincike kan hukumomi da ma’aikatun Gwamnatin Tarayya daga 2015 zuwa 2018.

A watan Yunin bana ne kuma kwamitin ya gabatar da rahoton binciken wata shidan da ya gudanar a kan hukumomin.

Sai dai a martanin sa, Akawun Majalisar Tarayya, Austen Adesoro, ya ce abubuwan da ake batu sun shafi shekarar 2019 ne kuma tuni an shawo kan su.