Home Labaru Yau Ne Kiristocin Duniya Ke Murnar Zagayowar Ranar Haihuwar Yesu Kiristi

Yau Ne Kiristocin Duniya Ke Murnar Zagayowar Ranar Haihuwar Yesu Kiristi

74
0

A ranar Asabar din nan ce Mabiya addinin Kirista suke gudanar da bukukuwan Kirsimeti wadda ake yi kowace ranar 25 ga watan Disamba.

Ana gudanar da bikin Kirsimeti ne domin tunawa da ranar haihuwar Yesu Almasihu.

Mabiya addinin Kirista a ko ina a fadin duniya na bayyana muhimmancin abubuwan al’ajabi da mu’ujizojin Yesu Isa Almasihu, wadanda malaman addinin Kirista suke jaddadawa ga mabiyan su a koda yaushe a cikin wa’azi.

Sun kuma yi amanna cewa wadannan mu’ujizoji wata babbar garkuwa ce a rayuwar su, muddin ba su saba wa abubuwan koyin da ya zo musu da su ba.