
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa gwamnatin sa ba za ta yi watsi da duk alkawuran da ta yi ba lokacin yakin neman zaɓa kafin cikar wa’adin sa.
Shugaban kasan ya bayyana haka ne a a sakon sa na Kirsimeti ga ’yan Najeriya, inda ya ce yana taya Kiristoci a Najeriya farin ciki kamar sauran mabiya a duniya don gudanar da bikin a wannan shekarar.
A cikin saƙon, shugaba Buhari ya roƙi ƴan Najeriya su yi rigakafin korona domin rage bazuwar annobar, ya kuma taɓo batun tsaro inda ya ce duk da nasarorin da jami’an tsaro suka samu amma har yanzu akwai ƙalubale.
Ya yi kira ga ƴan Najeriya su yi imani da kuma ɗaukar abubuwan da ke faruwa a matsayin wani lokaci da zai wuce, kamar sauran yanayi marar daɗi a tarihin ƙasa.
Ya ce gwamnatin sa ba za ta yi watsi da alƙawullan da ta yi wa ƴan Najeriya ba.
You must log in to post a comment.