Home Labaru Yau Ake Cika Shekara 10 Da Kisan Shugaba Gaddafi Na Libya

Yau Ake Cika Shekara 10 Da Kisan Shugaba Gaddafi Na Libya

15
0

Yau ake cika shekara 10 da kisan tsohon shugaban kasar Libya Moamer Gaddafi bayan juyin-juya halin kasar da ya juye zuwa rikici tare da yin awon gaba da kujerar mulkin sa.

Rikicin na Libya da ya samu goyon bayan manyan kasashen duniya da kungiyar tsaro ta NATO, masana na ganin shi ya assasa tashe-tashen hankula da ma bazuwar makamai a nahiyar Afrika.

Moamer Gaddafi wanda ya mulki Libya har tsawon shekara 42 tun daga 1969 bayan karbe mulki daga tsarin sarakunan gargajiya da kasar ke kai a baya, gabanin shekara ta 2011 da kasashen duniya suka yiwa gwamnatin sa taron dangi, kisan sa ya gaza taimakawa wajen tabbatar da Demokradiyya, batun da ke matsayin farfagandar da aka yi amfani da ita wajen samun goyon bayan ‘yan kasar a hambarar da mulkin na sa.

A ranar 20 ga watan Oktoban shekarar ta 2011 ne sojojin Amurka da kawayen ta suka bi sawun shugaba Gaddafi har zuwa mahaifar sa Sirte tare da kashe shi a tsakar titi baya ga jan gangar jikin sa a tsakar kasuwa.

Har zuwa yanzu Libya ta gaza murmurowa daga illar da hambarar da gwamnatin Gaddafi ta haifar mata, ba kadai ta bangaren tsaro ba har da tattalin arziki da kuma tsanantar rayuwa sabanin sassaukar rayuwa da ‘yan kasar ke yi a gwamnatin sa.