Home Labaru Modric Ya Soki Shirin Fifa Na Mayar Da Gasar Cin Kofin Duniya...

Modric Ya Soki Shirin Fifa Na Mayar Da Gasar Cin Kofin Duniya Duk Shekaru 2

10
0

Dan wasan tsakiya na Real Madrid, Luka Modric ya soki yunkurin hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA na kokarin mayar da gasar cin kofin Duniya duk bayan shekaru 2 sabanin 4 da aka saba.

A cewar dan wasan maimakon yunkurin FIFA na fara tuntubar manajojin kassahe kan matakin, kamata ya yi ta fara tuntubar ‘yan wasa kasancewar su abin ya fi shafa kai tsaye.

A ranar Litinin ne FIFA ta sanar da cewa za ta fara wata tattaunawa da masu horar da ‘yan wasan kasashe daga yau talata don jin ra’ayoyin su game da mayar da tsarin gudanar da gasar duk bayan shekara biyu.

Modric wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or bayan kai Croatia ga wasan karshe na cin kofin Duniya a shekarar 2018 da ya gudana a Rasha ya ce baya tunanin akwai ‘yan wasan da za su goyi bayan yunkurin na FIFA.

Acewar Modric mai shekaru 36 wanda ke amsa tambaya yayin taron manema labarai gabanin wasansu na yau da Shaktar Donetsk karkashin gasar cin kofin zakarun turai ya bayyana cewa sauya lokacin gasar zai rage mata kima da kuma karsashi.

Baya ga ‘yan wasan da ke sukar yunkurin na FIFA, su kan su manyan hukumomin wasanni na Duniya da suka kunshi hukumar kwallon kafar Turai UEFA da takwarar ta ta kudancin Amurka CONMEBOL baya ga kwamitin shirya wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya Olympics sun yi kakkausar suka ga FIFA kan kokarin sauya fasalin gasar wadda aka saba gudanar da ita duk bayan shekaru 4 fiye da shekaru 90 da suka gabata.