Home Labaru Mali Za Ta Yi Sulhu Da Al-qaeda

Mali Za Ta Yi Sulhu Da Al-qaeda

15
0

Hukumomin kasar Mali sun nemi babbar kungiyar musulunci ta kasar ta bude zaman tattaunawa da shugabannin kungiyar al -Qaeda ta yankin, a wani mataki na kawo karshen rikicin da ke zubar da jini tsawon shekaru a kasar.

A baya dai hukumomin Malin sun amince da ra’ayin tattaunawar bayan samun kwanciyar hankali a yunkurin ayyukan wanzar da zaman lafiya da kungiyoyin cikin gida ke yi, yayin da lamuran tsaro ke tabarbarewa sakamakon hare-haren kungiyoyin masu kishin addini.

Sai dai wannan sabuwar sanarwa da ke neman sake zaman sulhu da ma’aikatar addinin kasar Mali ta fitar, na zama mafi girman matakin shawo kan matsalar tsaro da ke addabar kasar, amma matakin na fuskantar zazzafar adawa daga kasar Faransa, inda Shugaba Emmanuel Macron ya fada a watan Yuni cewa bai zai cigaba da timakawa Mali da sojoji ba indai za ta yi sulhu da ‘yan ta’adda.