Home Labaru Ilimi Yarjejeniya: Kungiyar ASUU A Taraba Ta Janye Yajin Aikin Da Ta Shiga

Yarjejeniya: Kungiyar ASUU A Taraba Ta Janye Yajin Aikin Da Ta Shiga

438
0
# DaDumiDuminsa: MALAMAN JAMI’O’I SUN FARA YAJIN AIKI A NAJERIYA
# DaDumiDuminsa: MALAMAN JAMI’O’I SUN FARA YAJIN AIKI A NAJERIYA

Kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya ASUU reshen jihar Taraba ta janye yajin aikin da ta shiga a jami’ar jihar.

Kungiyar ta janye yajin aikin ne bayan yarjejeniyar da ta kulla tsakaninta da gwamnatin jihar.

Shugaban Kungiyar ta reshen jami’ar Dr. Samuel Shika, ya bayyana hakan jim kadan bayan ganawar su a Jalingo.

Shika, ya ce sun karbi tayin da gwamnatin tayi masu na bukatun su wanda dalilin hakan ne yasa suka janye yajin aikin.

Kungiyar ta umurci ‘ya’yan ta da su koma bakin aiki, kana daliban jami’ar su dawo makaranta don cigaba da karatu.

Leave a Reply