Home Labaru Makomar Ambode: Ana Zargin Yaran Tinubu Da Fara Kulle Kulle

Makomar Ambode: Ana Zargin Yaran Tinubu Da Fara Kulle Kulle

1076
0
Akinwunmi Ambode, Gwamnan Jihar Legas

Alamu na nuna  cewa tsohon gwamnan jihar Legas Akinwunmi Ambode, zai zamo daya daga cikin sababbin yan majalissar zartarwa ta tarayya.

Sai dai wasu rahotanni na cewa  mabiya bayan jigo a jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinibu, sun fara kulla hana a nada Ambode a matsayin minista.

Wani babban dan kungiyar Mandate, ya ce lokacin da Ambode, yake gwamna ya ta’azzari ‘yan jam’iyyar dayawa a Legas, saboda haka, akwai bukatar su dau fansa.

Haka zalika, ‘yan jam’iyyar a Legas sun fara shirye shiryen tuhumar Ambode, a hukumar EFFC a bisa zargin sa da handame kudin jihar.

Ambode, ya dawo Najeriya yan kwana biyu da suka wuce daga kasar Faran sa tun sadda ya bar kasar cikin watan Mayun wannan shekarar.

Wata majiya daga jam’iyyar ta ce Ambode, ya yi kokarin lalata jam’iyyar, inda majiyar tace bayan baya ganuwa, ya kuma soke kwantiragin da aka ba wasu yan jam’iyyar sa’annan ya kawo wasu kamfanoninshi ya basu.