Home Labaru Zaben 2019: Da Alamun Nasara A Karar Da Aka Kai Masari –...

Zaben 2019: Da Alamun Nasara A Karar Da Aka Kai Masari – Lauyan PDP

577
0

A cigaba da sauraron karar da jam’iyyar PDP ta shigar a gaban kotun sauraran kararakin zabe da ke Katsina an fara gabatar da shaidu dangane da rashin ingancin zaban gwamna da ya gabata wanda jam’iyyar PDP ta yi zargin an tafka magudi.

Sanata Yakubu Lado Danmarke, na jam’iyyar PDP da jam’iyya suka shigar da karar inda suke qalubalantar nasarar da gwamna Aminu Bello Masari, ya samu wanda hakan ya kara tabbatar da shi a matsayin zababan gwamna a karo na biyu a karkashin jam’iyyar APC.

Sai dai lauyan da ke jagorantar wannan shari’a a bangaran jam’iyyar Adawa ta PDP Gordy Uche, ya bayyanawa manema labarai cewa bisa ga yadda suke ganin wannan shari’a na tafiya akwai alamu nasara so sai.

Lauyan yace akwai abubuwa mahimahimcin a wannan shari’a da ya kama jama’a su sami wanda da shi ne suke sa ran za su samu nasara wajan wannan shari’a da ake fafatawa.Sai dai kuma da aka tuntubi bangaran gwamnati wanda sune aka kara, daya daga cikin jagorarin shari’a a bangaran gwamnati Ernest Obunidike, ya ce wanda suke karewa yana da takardun yin takarar gwamnan jihar Katsina kuma ya yi takara sau biyu ya ci zabe saboda haka ya cancanta.

Leave a Reply