Home Labaru Yara Kanana Na Bata-Dabo A Jihar Jigawa – Gwamna Badaru

Yara Kanana Na Bata-Dabo A Jihar Jigawa – Gwamna Badaru

67
0

Gwamna Muhammad Badaru na Jihar Jigawa, ya yi Kira ga Iyaye da al’umma su gaugauta sanar da hukumomi idan sun gani wata bakuwar fuska ta na shawagi a yankunan su.

Muhammad Badaru ya yi kiran ne, bayan samun rahotannin yadda kananan yara ke bata-dabo a fadin Jihar Jigawa.

A cikin wata sanarwa da Kakakin gwamna Badaru Habibu Kila ya fitar, ya ce gwamnan ya bukaci iyaye da sauran Jama’a su farga, su kuma rika sanin zirga-zirgar ‘ya’yan su don kada su fada hannun muggan mutane.

Kakakin rundunar ‘yan Sanda na jihar Jigawa Lawan Adam ya tabbatar da matsalar bacewar yara a Jihar, amma ya ce ‘yan Sanda su na tattara alkaluman yawan adadin yaran da su ka bace zuwa yanzu.