Home Labaru Kiwon Lafiya Gwamnati Ba Za Ta Yi Sanyi Wajen Tilasta Wa Mutane Yin Riga-Kafin...

Gwamnati Ba Za Ta Yi Sanyi Wajen Tilasta Wa Mutane Yin Riga-Kafin Korona Ba – Boss

14
0

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, ya ce gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tilasta mutane musamman ma’aikatan gwamnati yin allurar riga-kafin korona ba.

Boss Mustapha ya bayyana haka ne, a wani taron da kwamitin kula da harkokin cutar korona na gwamnatin tarayya ya yi da manema labarai a Abuja.

Ya ce rahotanni sun nuna cewa, cutar korona ta cigaba da yaduwa a wasu kasashen Turai saboda rashin yi wa mutane allurar riga-kafin ta.

Boss Mustapha, ya ce sun kuma samu rahoton cewa cutar ta cigaba da yaduwa a wasu kasashen da su ka yi wa mutanen su allurar riga-kafin, yayin da a nan Nijeriya cutar ke ci-gaba da kisan mutane.