Home Labaru Raddi: Ba Mu Ce Za Mu Kori Mata ‘Yan Sanda Masu Auren...

Raddi: Ba Mu Ce Za Mu Kori Mata ‘Yan Sanda Masu Auren Farar Hula Daga Bariki Ba -Sufeto Janar

70
0

Shugaban rundunar ‘yan Sandan Nijeriya Usman Alkali Baba, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa Rundunar za ta fitar da jami’an ‘yan sanda mata masu auren fararen hula daga barikonin da su ke zama.

Wasu kafafen yaɗa labarai dai sun ruwaito cewa, an ba duk wata jami’ar ‘yar sanda da ke zama a barikin Enugu wa’adin ta fita daga barikin daga nan zuwa watan Janairu na shekara ta 2022.

A cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya Frank Mba ya fitar a Abuja, shugaban ‘yan sandan ya ce labarin kanzon-kurege ƙaƙale, kuma rashin adalci ne da nuna bambanci idan aka kori ‘yar sanda mai auren farar hula daga barikin ‘yan sanda.

Usman Alkali Baba, ya ce ‘yan sanda maza da mata duk ɗaya ne bisa dokar Nijeriya, don haka ya ce babu wani banbanci a tsakanin su ta fuskar aiki, don haka ya umarci Babban Jami’in Bincike na Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, ya gaggauta gudanar da bincike domin gano wadanda su ka buga takardar.