Home Labaru Kiwon Lafiya ‘Yar shekara 10 ta warke daga coronavirus a Najeriya

‘Yar shekara 10 ta warke daga coronavirus a Najeriya

746
0
Cikin mutum 2 da suka warke daga cutar a Najeriya har da yarinya 'yar shekara10.
Annobar coronavirus a Najeriya ta fi kamari a jihar Legas, inda a nan aka fara samun bullarta a kasar.

An sallami karin wasu mutum 2 da suka warke daga cutar coronavirus a Najeriya.

A cikin wata sanarwar da ya wallafa a shafinsa a yammacin Litinin, Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya ce cikin wadanda aka sallaman har da wata yarinya ‘yar shekara 10.

Gwamnan ya ce an sallami matan su biyu ne daga asibitin killace masu dauke da cutar coronavirus da ke Yaba, bayan an tabbatar sun rabu da cutar.

A cewarsa sau biyu sakamakon gwajin da aka yi wa matan a karshe-karshen nan ke nuna cewa ba su duke da kwayar cutar.

Da yake bayyana farin cikin samun karuwar masu warkewa daga cutar, Sanwo-olu ya kuma kirayi jama’ar jihar da su bi umurni da shawarwarin masana, da kuma ba wa jami’ai hadin kai domin a yi nasarar shawo kan cutar a jihar.

A jihar Legas ne aka fara samun bullar cutar coroanvirus a Najeriya, kuma a nan cutar ta fi kamari, inda kawo yanzu mutum fiye da 120 ne suka kamu da cutar jihar.

Sama da mutum 25 sun warke daga cutar da ta kama mutum fiye da 230 a Najeriya, baya ga wasu mutum 5 da ta yi sanadiyyar mutuwarsu.