Home Labaru Buhari zai ciwo bashin tiriliyan 3.2 don yakar COVID-19

Buhari zai ciwo bashin tiriliyan 3.2 don yakar COVID-19

1920
0
Najeriya na sa ran shigowar wani bangare na rancen nan da mako shida
Najeriya na sa ran fara shigowar wani bangare na kudaden da za ta yi amfani da su domin farfado da tattalin arzikinta da annobar coronavirus ya daidaita, nan da mako shida

Najeriya za ta ciwo bashin fiye da dala biliyan 7, kimanin naira tiriliyan 3.2 kenan, domin farfado da tattalin arzikin kasar da annobar cutar coronavirus da durkusar.

Tuni Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta mika wa Asusun ba da Lamuni na Duniyan IMF, bukatarta na neman rancen gaggawa na dala biliyan 3.4 domin farfado da tattalin arzikin kasar.

Ministar Kudi Zainab Ahmed ta ce Najeriya na sa ran shigowar kudaden daga IMF a cikin mako shida masu zuwa, domin rage illar da annobar cutar ta yi wa tattalin arzikin kasar.

Yawan kudaden da kasar za ta karbo ya daga IMF din ya yi daidai da adadin kudin da Najeriya ke bayarwa a matsayin gudummuwarta ga IMF din.

Da take bayyana haka a lokacin bude gidauniyar tara naira biliyan 500 domin yakar cutar coronavirus a Najeriya, Ministar ta ce, Gwamnatin Tarayya na za ta karbo karin rancen dala bilyan 2 daga Bankin Duniya.

Ministar ta kara da cewa a karin yunkurin gwamanti ta rage mummuntar tasirin da annobar ta yi w tattalin arzikin Najeriya, gwamanti za ta kuma ranto dala biliyan 1 daga Bankin Kula Kasashen Afirka.

Zainab Ahmed ta ce rancen bai shafi dala miliyan 150 da ke asusun ajiya na SWF na Najeriya ba.

A jawabinta, ministar ta ce IMF ta amince kowace kasa na iya karbar rancen gaggawa domin farfado da tattalin arzikinsu da annobar ta shafa, matukar abin da suke nema bai wuce abin da ta ke ba wa asususun gudummuwa ba.

Sannan IMF ba ta gindaya wa kasashen da za su karbi rancen wani sharadi ba.

Zainab Ahmed na cewa daga cikin kudaden da gwamnati za ta karbo rance daga kasashen duniya, za a samar wa mataka 1,000 aikin yi, a kowacce daga cikin kananan hukumomi 774 da ke fadin Najeriya.

Karbar rancen na zuwa ne a daidai sadda mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ke cewa basukan da kasar ta ciwo sun yi mata yawa.