Home Labaru ‘Yancin Addini: Sarkin Musulmi Ya Yi Wa Kungiyar Kiristoci Ta Nijeriya Raddi

‘Yancin Addini: Sarkin Musulmi Ya Yi Wa Kungiyar Kiristoci Ta Nijeriya Raddi

429
0
‘Yancin Addini: Sarkin Musulmi Ya Yi Wa Kungiyar Kiristoci Ta Nijeriya Raddi
‘Yancin Addini: Sarkin Musulmi Ya Yi Wa Kungiyar Kiristoci Ta Nijeriya Raddi

Mai alfarma sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya maida martani game da ikirarin kungiyar kiristoci ta Nijeriya CAN, wadda ta kafa hujja da wani rahoton Amurka ta ce Kiristocin Nijeriya su na fuskantar muzgunawa.

Kungiyar CAN dai ta goyi bayan wani rahoton Amurka da ya sa Najeriya a jerin kasashen da ke hana ‘yancin gudanar da addini.

Sai dai yayin da yak e maida martani, sarkin Musulmi ya ce ya girgiza matuka da yadda kungiyar ta goyi bayan rahoton Amurka, har ma da karin kafa wasu hujjoji a kan yadda ake cin mutuncin mabiya addinin Kirista.

Ya ce ko kadan rahoton Amurka ba abin karba ba ne, domin ba za a iya sanya Nijeriya a sahun kasashen da ke zuba ido ana cin mutuncin wani addini ba.