Home Labaru Kyautar Kirsimeti: Oshiomhole Ya Watsa Wa Gwamna Obaseki Kasa A Ido

Kyautar Kirsimeti: Oshiomhole Ya Watsa Wa Gwamna Obaseki Kasa A Ido

228
0
Kyautar Kirsimeti: Oshiomhole Ya Watsa Wa Gwamna Obaseki Kasa A Ido
Kyautar Kirsimeti: Oshiomhole Ya Watsa Wa Gwamna Obaseki Kasa A Ido

Shugaban jam’iyyar APC Kwamred Adams Oshiomhole, ya ki karbar kyaututtukan Kirsimeti da gwamnatin jihar Edo ta aike ma shi.

Mai ba gwamnan jihar shawara ta fuskar yada labarai Crusoe Osage ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce an maida kyaututtukan kayan Kirsimeti da aka aike wa Oshiomhole.

Ya ce ‘yan aiken sun ce, sun tarar da mahaifiyar Oshiomole ne, amma ta shaida masu cewa dan ta ba zai amshi kyaututtukan ba, wadanda su ka hada da shanu hudu da buhuhunan shinkafa goma.

Osage, ya ce rabon kayayyakin Kirsimeti abu ne da gwamnatin jihar ta saba yi duk shekara a matsayin hanyar nuna so da karfafa zumunci tsakanin gwamnatin da mutane.

Ya ce Obaseki da Oshiomhole sun fada rikicin siyasa kan manufar gwamnan ta maida hankali ga jin dadin mutane fiye da komai, domin ya na adawa da ba ‘yan siyasa filin kashe-mu-raba da kudin jihar.