Home Labaru Kasuwanci Yanayin Kasuwa Ya Haifar Da Ƙarin Farashin Fetur – Kyari

Yanayin Kasuwa Ya Haifar Da Ƙarin Farashin Fetur – Kyari

39
0

Shugaban Kamfanin Fetur na Nijeriya NNPCL Mele Kyari,
ya ce yanayin kasuwa ne ya haifar da ƙarin farashin man fetur
da aka fuskanta yanzu haka.

Mele Kyari ya bayyana haka ne, yayin ganawa da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda ya ce sakar wa ɓangaren mai mara da aka yi zai sa a riƙa fuskantar hawa da saukar farashin man a lokaci- lokaci.

Ya ce batun ƙarin farashin man fetur daga Naira 540 zuwa Naira 617 da aka fuskanta ba wai don ƙarancin fetur ba ne, ya na mai tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa akwai man wadataccen man fetur.

Mele Kyari ya kara da cewa, sashen kasuwanci na kamfanin NNPC ke da alhakin kula da farashin mai, kuma su kan daidaita farashin ne bisa la’akari da yanayin kasuwar man.

Leave a Reply