Rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara, ta kafa kwamitin
bincike a kan yadda wasu ‘yan sanda su ka kama motar
shugaban jam’iyyar APC na jihar Alhaji Tukur Danfulani tare
da tsare direbansa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan ASP Yazid Abubakar ya bayyana haka a Gusa, inda ya ce rundunar ba ta da masaniya a kan lamarin, amma za ta cigaba da gudanar da cikakken bincike a kan wadanda ake zargi.
Ya ce ba su samu wani rahoto mai kama da haka ba, amma kwamishinan ‘yan sanda na jihar Muhammad Bunu ya gayyaci dukkan bangarorin da abin ya shafa domin gudanar da bincike.
Rundunar ‘yan sandan, ta maida martani a kan wata sanarwa da Sakataren yada labarai na Jam’iyyar APC na Jihar Yusuf Idris ya fitar, inda ya zargi cewa wasu ‘yan sandan da ke aiki a gidan gwamnati Gusau sun yi wa direban su wulakanci tare da kama shi da tsare shi na tsawon sa’o’i.