Home Labaru ‘Yan Ta’addan Boko Haram 17,000 Su Ka Mika Wuya Kawo Yanzu –...

‘Yan Ta’addan Boko Haram 17,000 Su Ka Mika Wuya Kawo Yanzu – Kwamdanda

14
0

Tiyata Kwamanda na rundunar ‘Operation Hadin Kai’ Christopher Musa, ya ce adadin mayakan Boko Haram da su ka mika wuya ya kai dubu 17.

Musa ya bayyana hakan ne, yayin da ya kai ziyara wajen shugabannin hukumar ci-gaban Yankin Arewa maso gabas, NEDC, inda ya ce adadin ya hada da mayakan da iyalan su da kuma wadanda aka tilasta ma shigar harkar Boko Haram.

Ya ce adadin masu mika wuyan a kullum karuwa yak e, don haka akwai bukatar hukumar NEDC ta taimaka wajen kula da su.

Kwamanda Musa ya kara da cewa, yan ta’addan ISWAP ba su jin dadi a kan mika wuyan da ‘yan Boko Haram ke yi, kuma hakan ya sa su ka kafa runduna ta musamman domin hana mayakan gudu.