Home Labaru Gwamnatin Gombe Ta Zargi Danjuma Goje Da Rura Rikicin Siyasa A Jihar

Gwamnatin Gombe Ta Zargi Danjuma Goje Da Rura Rikicin Siyasa A Jihar

19
0

Gwamnatin jihar Gombe, ta soki lamirin Sanata Danjuma Goje bisa rikicin da ya auku a jihar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Kwamishanan labarai na jihar Julius Ishaya Lepes, ya ce Danjuma Goje da kan sa ne ya haddasa rikicin, domin tun farko halin sa kenan ya tattara ‘yan Kalare a duk lokacin da zai shiga jihar Gombe.

Ya ce tsohon gwamnan ya saba ya tattara ‘yan Kalare daga kananan hukumomi daban-daban da sunan masu rakiyar sa zuwa garin Gombe, kuma abin da ya faru kenan a karamar hukumar Yamaltu Deba.

Julius Ishaya, ya ce har yanzu Danjuma Goje ya na da burin tura ‘yan kalare domin su hana jama’a zaman lafiya a jihar Gombe, don haka gwamnati ba za ta zuba ido wasu ‘yan siyasa su tada rikicin da zai haddasa asarar rayuka ba.