Home Labaru El-Rufai Ya Nada Farfesa Daga Ingila A Matsayin Mai Bada Shawara

El-Rufai Ya Nada Farfesa Daga Ingila A Matsayin Mai Bada Shawara

27
0

Gwamnatin jihar Kaduna, ta bada sanarwar nada Farfesa Rajneesh Narula a matsayin mai bada shawara a hukumar tsare-tsare da kasafin kudi na jihar.

Rajneesh Narula dai zai taimaka wa Gamnatin Kaduna wajen bada shawara a kan yadda za a dabbaka dabarun kasafin kudi, sannan zai bada gudumuwa wajen ganin tsare-tsaren gwamnati sun kai ga kananan hukumomi ta karkashin majalisar tsare-tsaren tattalin arziki.

Mai taimaka wa gwamnan jihar Kaduna ta fuskar yada labarai da sadarwa Muyiwa Adekeye ya bada sanarwar.

Rajneesh Narula dais hi ne shugaban cibiyar kula da harkokin kasuwanci ta kasashen Duniya a jami’ar Reading, kuma darakta a cibiyar Dunning a kasar Afrika ta kudu.