Home Labaru ‘Yan Siyasar Mali Sun Fara Shirin Zabe

‘Yan Siyasar Mali Sun Fara Shirin Zabe

100
0

Wani kawancen jam’iyyu siyasa 10 na kasar Mali ya yi watsi da bukatar gwamnatin soji ta kasar ta ci gaba da zama kan madafun iko har zuwa shekara ta 2026.

Mai magana da yawun ‘yan siyasar Sekou Niame Bathily ya ce kawancensu na duba hanyoyin da zai fara yunkurin shirya zabe a kasar.

A karshen mako ne dai sojojin suka sanar da kungiyar bunkasa kasashen Afirka ta ECOWAS cewa za su dan yi jinkirin gudanar da zabe a Mali har zuwa nan da shekaru biyar sabanin farkon wannan shekara da muke ciki.

ECOWAS din ba ta kai ga ba su amsa ba a kan bukatar tasu. Sai dai ta yi barazanar sanya wa sojojin takunkumi idan har suka ci gaba da jinkirin gudanar da zaben. 

A ranar 9 ga wannan wata ne dai ECOWAS din za ta zauna don sanar da sabuwar matsayarta kan sojojin na Mali.

Ana dai zargin gwamnatin sojin da saba alkawuranta na cewa za ta gudanar da zabe cikin hantsari bayan juyin mulki har sau biyu da sojoji suka yi tun daga shekara ta 2020.

Leave a Reply