Home Labaru Pochettino Ya Ce Sai Messi Ya Warke Zai Koma Faransa

Pochettino Ya Ce Sai Messi Ya Warke Zai Koma Faransa

158
0

Dan wasan Paris Saint Germain Lionel Messi ya kebe kansa bayan da gwaji ya nuna cewa ya harbu da cutar Coronavirus.

Kungiyar ta PSG ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi a cewar Reuters.

Messi ya kebe kansa ne a kasarsa ta Argentina, kuma ba zai samu damar yin tafiya zuwa Faransa ba, sai gwaji ya nuna cewa ba ya dauke da cutar a cewar hukumomin kungiyar.

A cewar PSG, sauran ‘yan wasan da suka kamu da cutar akwai mai tsaron gida Juan Bernat, da mai tsaron raga na biyu Sergio Rico sai dan wasan tsakiya Nathan Bitumazala.

Wannan lamari ya faru ne yayin da PSG ke shirin karawa da Vanne a ranar Litinin a gasar French Cup.

Leave a Reply