Home Home Plateau: Duk Yan Bindigan Da Muka Kama A Jiha Ta Kwanan Su...

Plateau: Duk Yan Bindigan Da Muka Kama A Jiha Ta Kwanan Su Ya Kare- Gwamna Lalong

126
0

Gwamnan jihar Filato Simon Lalong, ya gargadi yan bindiga masu garkuwa da mutane su tattara komatsansu su bar jihar sa.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a cocin Catholic dake karamar hukumar Shendam a jihar Filato, inda ya ce duk wanda hukumomin tsaro suƙa kama, ba makawa zai fusakanci hukuncin kisa.
Ya kuma tabbatarwa mazauna jihar cewa gwamnatinsa za ta kara zage dantse wajen yaki da ta’addanci, musamman garkuwa da mutane wanda ya zama barazana da zaman lafiyar al’ummar jihar.
Ya ce za su kara kaimi wajen kawo karshen dukkan ayyukan ta’addanci, musamman garkuwa da mutane, wanda a yanzu ya zama barazana da zaman lafiya da tsaron al’ummar Filato da wasu sassan Najeriya.
Wannan gargaɗin da gwamna Lalong ya yi, ba zai rasa nasaba da harin sace mutane da ake fuskanta a wasu sassan jihar Filato kwanan nan.
A ranar 26 ga watan Disamba, wasu yan bindiga sun sace babban basaraken garin Gindiri, dake karamar hukumar Mango, Charles Mato Dakat, a gidansa, amma daga bisani maharan sun sako basaraken bayan kwashe kwanaki hudu a hannun su.

Leave a Reply