Home Labaru ‘Yan Sandan Sun Ceto Matasa Da Ake Azabtarwa A Gidan-Mari A Kano

‘Yan Sandan Sun Ceto Matasa Da Ake Azabtarwa A Gidan-Mari A Kano

17
0

Jami’an ‘yan sanda sun ceto mutane 47 daga wani Gidan-Mari a jihar Kano.

Wurin dai, wanda ake kira gidan gyaran hali wuri ne da iyaye kan tura ‘ya’yan su masu miyagun dabi’u da shaye-shaye da aikata manyan laifuffuka.

Yayin da ‘yan sandan su ka kai samame, sun ceto mutane 47 duk maza, wadanda shekarun su ke tsakanin 14 zuwa 35 sanye da sarkoki sanna da alamun bugu a Jikin su.

Kakakin ‘yan sanda na jihar Kano Abdullahi Haruna ya shaidawa manema labarai cewa, an kama mutumin da ke da gidan kuma za a gabatar da shi kotu.

Gwamnatin jihar Kano dai ta haramta irin wadannan gidaje watanni 10 da su ka gabata, bayan an kai sameme a ire-iren gidajen da ake cin zarafi ko azabtar da mutane da sunan tarbiyya.