Home Labaru Kasuwanci Tsadar Burudo Da ‘Pure Water’ Ya Addabi Babban Birni Abuja

Tsadar Burudo Da ‘Pure Water’ Ya Addabi Babban Birni Abuja

17
0

Mazauna birnin Abuja da wasu sassan yankunan jihar Neja, sun shiga damuwa a kan sabon farashin Burodi da Ruwan Leda.

Rahotanni sun ce, an kara farashin duk da cewa wasu abubuwan ba su da alaka da rashin tsaro ko tsadar kayan masarufi da canjin Naira zuwa Dala.

Yanzu haka dai, Jakar ruwan leda da a ke saidawa a kan Naira 100, yanzu ya haura tsakanin Naira 200 zuwa N250, yayin da ake saida kwara daya a kan Naira 20.

Daya daga cikin masu buga ruwan leda Dasuma Friday, ya ce wasu abubuwan da ke janyo hauhawar farashin sun hada da tsadar buga ledar da kuma kudin wutar lantarki.

Tuni dai kungiyar masu buga ruwan leda ta fara yajin aiki, da nufin fahimtar da jama’a cewa kasuwancin ba zai dore ba sai sun yarda da canjin farashin.