Home Labaru Saboda A Murde Zaben Gwamna Ake Shirin Kafa Dokar Ta-Baci A Anambra...

Saboda A Murde Zaben Gwamna Ake Shirin Kafa Dokar Ta-Baci A Anambra – PDP

13
0
PDP

Jam’iyyar PDP ta yi gargadi dangane da kafa dokar ta-baci a jihar Anambra yayin da ake shirin gudanar da zaben sabon gwamnan jihar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar PDP Kola Ologbondiyan ya fitar, ya ce gwamnatin tarayya ta ma daina tunanin sa wata dokar ta-baci a jihar Anambra.

Kola Ologbondiyan, ya kuma zargi gwamnatin jam’iyyar APC da yunkurin tafka magudi a zaben ta yadda za ta kafa gwamnati a jihar Anambra.

Ya ce da gangan aka kirkiro duk rikice-rikicen da ke faruwa a jihar Anambra, kawai saboda jam’iyyar APC ta samu damar murde zaben ta kafa gwamnati.