Home Labaru ‘Yan Sandan Nijeriya Sun Bindige Mahaukaci Bayan Ya Fille Kan Wani Dattijo

‘Yan Sandan Nijeriya Sun Bindige Mahaukaci Bayan Ya Fille Kan Wani Dattijo

121
0

Wani magidanci mai suna David Shodola da ake zargin ya na
da tabin hankali, ya jefa garin Ipara da ke karamar hukumar
Remo ta Arewa a jihar Ogun cikin rudani, bayan ya fille kan
wani dattijo mai shekaru 84 Alfred Opadipe.

Wata majiya ta ce, tuni jami’an ‘yan sanda sun harbe mahaukacin bayan ya bijirewa kama shi.

Wani faifan bidiyo mai tsawon mintina tara da dakika takwas da aka yada a kafofin sada zumunta ya nuna gawar mahaukacin a kasa, sannan nesa da shi kadan ana ganin wani kai da ake zargin na dattijon da ya fille ne.

Wani ganau da ya yi magana a cikin faifan bidiyon, ya ce mahaukacin ne ya kashe dattijon wajen fille ma shi kai.

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sanda ta jihar Ogun Omotola Odutola, ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ta fitar a Abeokuta.

Odutola ta ce, rundunar ta samu kiran gaugawa daga wani mazaunin unguwar da lamarin ya faru, don haka aka tura ‘yan sanda a karkashin jagorancin jami’in ‘yan sanda na Isara CSP Bankole Eluyeru, inda ya yi yunkurin kama wanda ake zargin, amma ya yi amfani da adduna wajen kare kan sa ya tunkari jami’an tsaro da sauran mutane, lamarin da ya sa aka bindige shi har lahira.

Leave a Reply