Home Labaru Tinubu Na Neman Kare Kansa Daga Sammacin Da Atiku Ya Yanko Masa...

Tinubu Na Neman Kare Kansa Daga Sammacin Da Atiku Ya Yanko Masa A Amurka

173
0

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya shigar da buƙatar
soke sammacin da Atiku Abubakar ya yanko ma shi daga
wata kotu da ke Illinois a jihar Chicago ta ƙasar Amurka.

A ranar 11 ga watan Yuli ne Atiku Abubakar ya shigar da ƙara, ya na neman samun ƙarin bayani a kan bayanan karatun Tinubu a jami’ar jihar Chicago.

Daga cikin takardun da Atiku ya nema ta hannun lauyar sa Angela M. Liu, akwai shaidar shigar Tinubu jami’ar da ta ɗaukar sa, da kwanakin da ya yi har zuwa lokacin da ya kammala digiri.

Atiku Abubakar, ya kuma nemi sanin lambobin yabo da karramawar da Tinubu ya samu lokacin da ya ke karatu a jami’ar da dai sauransu, ya na mai cewa ya yanki takardar sammacin da aka aike wa Tinubu ne domin tabbatar da gaskiyar abubuwan da ya ke iƙirari.

Da yake maida martani a kan ƙarar, lauyan Tinubu Victor P. Henderson, ya buƙaci kotun ta yi watsi da ƙarar saboda babu wani alƙalin kotun da ya saurare ta, ya na mai iƙirarin cewa ƙarar ba ta inganta ba sakamakon kwanaki shida kacal da ake so wanda aka yi ƙarar ya bayyana gaban kotu, bai kai kwanaki 14 na ƙa’ida ba kamar yadda ya ke a sashe na 219 da 137 na dokokin kotun ƙoli ta Illinois.

Leave a Reply