Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna Mohammed
Jalige, ya ce rundunar ta yi nasarar kama wasu bata-gari da
barayin waya da masu tu’ammali da miyagun kwayoyi 207.
Mohammed Jalige, ya ce baya ga barayin waya da aka kama, jami’an tsaro sun kama wasu da dama masu yi wa mutane rufa-ido da katin ATM su damfare su.
Idan dai ba a manta ba, makonni biyu da su ka gabata, Jalige ya ce ‘yan sanda sun kama masu tada zaune tsaye a fadin jihar Kaduna har mutane 503
Ya ce a cikin su an kama ‘yan bindiga, da masu yi wa yan mata fyade, da ‘mashaya da barayin waya, kuma har bindigogi an kwato a hannun wadanda aka kama.














































