Home Labaru An Ceto Mutum 30 Daga Hannun Ƴan Bindiga A Kebbi

An Ceto Mutum 30 Daga Hannun Ƴan Bindiga A Kebbi

521
0

An ceto akalla mutane 30 da ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da
su a yankin Danko Wasagu da ke jihar Kebbi.

Waɗanda aka ceto kuwa sun fito ne daga garin Kontagora na jihar Neja da Danmari da Kaba da kuma Kajiji a jihar Zamfara da kuma Bena ta jihar Kebbi.

Shugaban karamar hukumar Danko Wasagu Alhaji Useni Aliyu Bena ya bayyana wa manema labarai haka.

Aliyu Bena, ya kuma yaba wa gwamnatin jihar Kebbi bisa yadda ta ke aiki da jami’an tsaro, tare da ba su tallafi domin ganin an fatattaki ‘yan bindigar da su ka addabi jihar da ma maƙwaftanta har aka kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su.

LEAVE A REPLY