Home Labaru ‘Yan Sanda Sun Kammala Bincike Kan Alasan Doguwa, Saura Fara Shari’a

‘Yan Sanda Sun Kammala Bincike Kan Alasan Doguwa, Saura Fara Shari’a

1
0

Shugaban Rundunar ‘yan sandan Nijeriya Usman Alƙali
Baba, ya kammala nazari da binciken kundin bayanan zargin
kisan ‘yan adawa da ake yi wa Shugaban Masu Rinjaye na
Majalisar Tarayya Alhassan Doguwa.

Tuni dai Alƙali Baba ya maida wa Gwamnatin Jihar Kano kundin domin a gurfanar da Alhassan Ado Doguwa a gaban kotu.

Tun farko dai ‘yan sanda ne su ka kama Ado Doguwa, inda su ka maka shi Kotun Majistare bisa zargin shi da kisan mutane uku a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Sai dai Alhassan Ado Doguwa ya zargi Kwamishinan ‘yan Sanda na Jihar Kano da yi masa rashin adalci tare da nuna ma shi ɓangaranci yayin da ya ke bincike a kan rikicin.

Tawagar binciken shugaban ‘yan Sandan da su ka karɓi kundin daga Kano, sun aika da sakamakon da su ka gano zuwa ga Antoni Janar kuma Kwamishinan Shari’a na jihar Kano Mai Shari’a Musa Lawan, abin da ya rage kawai shi ne gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da Ado Doguwa a tuhume
shi a kan zargin aikata babban laifi.