Gamayyar zaɓaɓɓun sanatocin yankin Arewa ta Tsakiya, sun
bayyana Sanata Sani Musa cewa shi su ke so ya zama
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.
Zaɓaɓɓun Sanatocin daga jihohin Neja da Benue da Filato da Nasarawa da Kogi da kuma Kwara, sun ce idan aka yi masu haka to an raba romon dimokraɗiyya tare da yankin su kenan.
Zaɓaɓɓen Sanata daga jihar Nasarawa Aliyu Wadada ya bayyana wannan matsaya, lokacin da ya yi wa manema labarai bayani bayan taron sanin makamar aikin da aka shirya wa zaɓaɓɓun ‘yan majalisa a Abuja.
Wadada, ya ce ya na tattaunawa da sauran sanatocin da aka zaɓa daga yankin domin su samu mukamin mataimakin shugaban majalisar dattawa.