Home Labaru ‘Yan Sanda Sun Kama Wani Mutum Bisa Zargin Sayar Da ‘Ya’Yansa Uku

‘Yan Sanda Sun Kama Wani Mutum Bisa Zargin Sayar Da ‘Ya’Yansa Uku

48
0

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Rivers, ta kama wani mutum bisa
zargin sa da saida ‘ya’yansa uku.

Yayin da ‘yan sanda ke gabatar da mutumin a ofishin su da ke tsohuwar GRA a jihar, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Grace Iringe-Koko, ta ce sun kama mutane masu yawa da ke harkar saida ƙananan yara a fadin jihar.

Mutumin mai suna Michael Charles, ya yarda da cewa ya saida ‘ya’yan sa, inda ya ce talauci da rashin halin ɗaukar nauyin ‘ya’yan ne ya sa shi ɗaukar wannan mataki.

Sauran mutanen da ke da hannu wajen saida yaran sun hada da wani likita da wani tsohon kansila.

Yayin da ta ke magana a madadin mahaifiyar yaran, kakar yaran ta ce surukin ta ya daɗe ya na saida ‘ya’yan da ‘yar ta ta ke haifawa, tare da yi mata ƙaryar cewa yaran mutuwa su ke yi a lokacin haihuwa.

Wata sanarwa da ‘yan sanda su ka fitar, ta ce bayanan da sun samu sakamakon kama wasu da ake zargi da safarar ƙananan yara ne ya kai su ga gano mutanen da wadanda su ke sayen jarirai, inda daya daga cikinn su mai suna Favour Amaewhule ta ce ta sayi jariri 1 a kan naira 700,000.

Leave a Reply