Home Labaru Ana Fargabar Mutuwar Tarin Mutane Bayan Ruftawar Bene Mai Hawa 20 A...

Ana Fargabar Mutuwar Tarin Mutane Bayan Ruftawar Bene Mai Hawa 20 A Lagos

14
0

Rahotanni daga jihar Lagos, sun bayyana yadda wani bene mai hawa 21 da ake tsaka da aikin ginin sa ya rufta, inda ake fargabar mutuwar tarin jama’a galibin ma’aikatan da ke tsakiyar da aiki.

Lamarin dai ya faru ne a anguwar Ikoyi da ke karamar hukumar Eti Osa, inda shaidun gani da ido su ka tabbatar da cewa mutanen da baraguzan ginin ya rufe da su za su iya haura 100, kuma galibin su masu aikin zuba kankare ne.

Har yanzu dai babu cikakken bayani a kan yawan mutanen da su ka rasa ran su ko kuma su ka jikkata, yayin da wata jita-jita ke cewa ginin mallakin wani na kusa ne da gwamnatin Nijeriya ne.

Ruftawar gine-gine dai ba sabon abu ba ne a Lagos, yayin da ake ci-gaba da samun karuwar masu gine-gine marasa inganci.