Home Labaru ‘Yan Sanda Sun Kama Matashin Mawaki Tekno A Legos

‘Yan Sanda Sun Kama Matashin Mawaki Tekno A Legos

1194
0

Jami’an ‘yan sanda sun kama matashin mawaki Tekno, sakamakon yin rawa da wasu mata kusan tsirara a cikin wata babbar mota a birnin Legas.

Motar dai ta na da gilashi mai haske a bayan ta, lamarin da ya ba mutane damar iya ganin masu rawar a lokacin da na’urar bada hannu ta tsaida su.

‘Yan sanda sun tabbatar da kama fitaccen mawakin, wanda cikakken sunan sa shi ne Augustine Kelechi, saboda yawo da mata kusan tsirara a yankin Lekki da ke birnin Lagos.

Mawakin, wanda ya fito a kundin wakar da mawakiyar Amurka Beyonce ta fitar kwanan nan, ya jefa mutane da dama cikin dimuwa, bayan ya shiga cikin wani abu da ya yi kama da tallar gidan rawa na tabara da a kan yi tsirara.

Matafiya a kan titi dai sun yi mamakin ganin sa ya na tikar rawa a motar, wadda ana iya ganin abin da ke faruw a cikin ta.