Home Labaru Jami’ar Bayero Ta Samu Lasisin Bude Gidan Talabijin Na Kan Ta

Jami’ar Bayero Ta Samu Lasisin Bude Gidan Talabijin Na Kan Ta

338
0

Hukumar kula da kafafen yada labarai ta Nijeriya NBC, ta ba jami’ar Bayero da ke Kano lasisin da zai ba ta damar kafa gidan talabijin.

Lasisin da jami’ar ta samu dai zai ba ta damar kafa gidan talabijin na kan ta, ta yadda za ta rika koyar da dalibai aikin yada labaran talabijin kamar yadda shugaban hukumar NBC Ishaq Kawu ya bayyana.

Yanzu haka dai jami’ar ta na da gidan rediyon da ke yada labarai daga harabar ta.

Shugaban sashen karatun gaba da digiri na jami’ar Farfesa Umar Pate ya shaida wa manema labarai cewa, sun samu tallafin kudaden gina dakin gabatar da shirye-shiryen gidan talabijin ne daga wasu kungiyoyi, ya na mai cewa za a yi amfani da lasisin wajen horar da dalibai aikin jarida na binciken-kwakwaf.