Home Labaru Kotu Za Ta Saurari Karar DSS Ta Tsare Sowore A Ranar Alhamis

Kotu Za Ta Saurari Karar DSS Ta Tsare Sowore A Ranar Alhamis

231
0
Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya, DSS
Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya, DSS

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta sa ranar 8 ga watan Agusta domin yanke hukunci a kan karar da hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta shigar na tsare jagoran zanga-zangar juyin-juya-hali Omoyele Sowore na tsawon kwanaki 90 zuwa lokacin da za ta kammala bincike.

Mai shari’a Taiwo Taiwo ne ya dage sauraren shari’ar, domin ba shi damar kallon faiffan bidiyon da hukumar DSS ta sa a cikin karar da ta shigar.

Da farko dai lauyan hukumar DSS G. O. Abadua, ya ce an shigar da karar ne domin nema tsare Sowore na tsawon sama da sa’o’i 48 da doka ta bada, biyo bayan kamun da aka yi ma shi.

Jami’an hukumar DSS ne su ka kama Sowore, wanda ya kasance mawallafin jaridar Sahara Reporters, kuma dan takarar shugan kasa na jam’iyyar AAC a zaben shekara ta 2019.

Hukumar DSS ta ce, an kama Sowore ne bisa kokarin jan ragamar zanga-zangar juyin-juya-hali na gama-gari a kan gazawar gwamnatin Nijeriya.