Home Home ‘Yan Sanda Sun Kama Fasto Kan Garkuwa Da Kansa Don Karɓar Kuɗi...

‘Yan Sanda Sun Kama Fasto Kan Garkuwa Da Kansa Don Karɓar Kuɗi A Wajen Mabiyan Sa

26
0
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Filato, ta kama wani fasto bisa zargin sa da yin garkuwa da kan sa domin karɓar kuɗi a wajen mabiyan sa.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Filato, ta kama wani fasto bisa zargin sa da yin garkuwa da kan sa domin karɓar kuɗi a wajen mabiyan sa.

A cikin wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar, ta ce Faston mai suna Albarka Bitrus, ya haɗa baki da wasu ne ya ɓoye kan sa domin ya karɓi kuɗin fansa a wajen mabiyan sa.

Sanarwar ta ce, an kama faston tare da waɗanda ya haɗa hannu da su wajen aikata wannan laifin, bayan sun samu bayanan sirri da ke cewa tuni mabiya cocin sun biya naira dubu 600 a matsayin kuɗin fansa.

Ta ce bayan samun labarin garkuwa da faston, da kuma biyan nairan dubu 400 da naira dubu 200 daban-daban a matsayin kuɗin fansa domin sakin sa, sai lamarin ya fara sa shakku a zukatan mutane.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, bayan an samu bayanan sirri, sai shugaban ‘yan sanda na Nassarawa Gwong ya gayyaci faston, nan take aka fara gudanar da bincike, inda faston ya tabbatar da cewa ya haɗin baki ne da wasu ne domin ya karɓi kuɗi a wajen mabiyan sa.