Home Home Shugaban DSS Ya Magantu Kan Rikicin Matarsa ​​Da Abba Gida-Gida Da Ya...

Shugaban DSS Ya Magantu Kan Rikicin Matarsa ​​Da Abba Gida-Gida Da Ya Barke A Kano

98
0
Shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS Yusuf Magaji Bichi, ya ce makiya ne su ke kokarin bata ma shi suna da na  iyalan sa saboda ya ki amincewa da sauya wasu muhimman batutuwan mulki da harkokin kasa.

Shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS Yusuf Magaji Bichi, ya ce makiya ne su ke kokarin bata ma shi suna da na  iyalan sa saboda ya ki amincewa da sauya wasu muhimman batutuwan mulki da harkokin kasa.

Yusuf Bichi, ya zargi kungiyoyin fararen hula da kungiyoyi masu zaman kan su da shirya wannan makircin, ta hanyar gudanar da tarurrukan manema labarai da zanga-zanga a kan tituna domin bata ma shi suna.

A baya dai rahotanni sun ce an samu sabanin rashin fahimta a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, tsakanin uwargidan sa A’isha Bichi da Abba Gida-gida na jam’iyyar NNPP, yayin da ta hana shi hawa jirgi.

Rikicin dai ya samo asali ne, bayan ayarin motocin Abba Gida-gida sun janyo wa ayarin A’isha Bichi tsaiko wajen shiga dakin manyan baki na filin jirgin, inda jami’an tsaron ta su ka shiga cikin lamarin domin bude hanyar, lamarin da ya kai ga cece-ku-ce tsakanin jami’an tsaro da mataimakan dan takarar gwamnan.

Da yake maida martani kan lamarin ta bakin mai magana da yawun hukumar DSS Peter Afunanya, Yusuf Bichi ya ce ma’aikatar sa ta bankado tsare-tsare da wasu ‘yan siyasa da wasu ‘yan bangar siyasa da ke cikin gwamnati da wajen ta ke kokarin daukar nauyi domin bata ma shi suna.

Leave a Reply