Home Ilimi ‘Yan Sanda Sun Fara Binciken Tambaɗar Da Daliban Makarantar Chrisland Su Ka...

‘Yan Sanda Sun Fara Binciken Tambaɗar Da Daliban Makarantar Chrisland Su Ka Yi

116
0

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Legas, ta fara gudanar da binciken bidiyon wata ‘yar makarantar attajirai da ke Legas, wadda aka nuno ta tsirara tare da wani matashi su na fasikanci cikin wani Otal a Dubai.

Kakakin ‘yan sanda na jihar Legas Benjamin Hundeyin, ya ce
‘yan sanda sun fara bincike a kai, kuma za su tabbatar da sun
bankaɗo abin da ya ya auku a cikin bidiyon.

Tun farko dai gwamnatin jihar Legas ta sanar da rufe makarantar
har sai an gama bincike, sannan ta gargaɗi mutanen da su ka
mallaki bidiyon kada su rika yada shi, don haka idan aka kama
wani ya yi haka za a maka shi kotu.

Wata majiya ta ce, daliban sun tafi kasar Dubai ne domin
halartar wata gasar makarantu.