Hadin gwiwar ‘yan sandan kasa da kasa da takwarorin su na kasar Mali sun ceto mutane 64, mafi akasarin su manyan mata da kanana daga masu safarar mutane da ke bautar da su.
‘Yan sandan na kasa da kasa sun ce, an yi safarar wadanda aka ceton ne zuwa birnin Bamako, daga kasashen Najeriya, Burkina Faso, da Mali, inda ake tilasta masu yin karuwanci da bauta da kuma bara a mashaya da gidaje da kuma wuraren hakar ma’adanai.
Tuni dai jami’an tsaron sun kama wasu mutane 4 da ake zargi da safarar mutanen, yayin da aka baza komar kamo wadanda su ka tsere.
Wani rahoton hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya ya ce, sama da ‘yan ci-rani dubu 160 ne su ka shiga Mali ko aka yi safarar su, a tsakanin watan Yuli na shekara ta 2016 zuwa karshen watan Janairun shekara ta 2019.
You must log in to post a comment.