Home Labaru ‘Yan Boko Haram Na Rike Da Wasu Kananan Hukumomi Biyu A Nijeriya

‘Yan Boko Haram Na Rike Da Wasu Kananan Hukumomi Biyu A Nijeriya

986
0

Wasu rahotanni daga kungiyoyin da ke sa-ido a kan batutuwan da su ka jibanci ayyukan jin-kai a Nijeriya, sun gano cewa akalla mutane miliyan 1 da dubu 200 ne Boko Haram ta yi wa kofar-rago a kananan hukumomi biyu da ke Jihar Borno.

Al’umomin yankunan da lamarin ya shafa dais u na cikin wani halin rashin tabbas dangane da batun tsaro, a daidai lokacin da hukumomi ke ci-gaba da cewa su na dab da kawo karshen kungiyar Boko Haram.

A dan tsakanin nan dai mayakan kungiyar Boko Haram sun kai wasu jerrin hare-hare tare da kisan sojojin Nijeriya.