Home Labaru ‘Yan Sanda A Katsina Sun Kama Wani Yaro Dan Shekara 14

‘Yan Sanda A Katsina Sun Kama Wani Yaro Dan Shekara 14

14
0

Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta ce ta kama wani yaro ɗan ƙasa da shekara 20 da ake zargi da shiga ayyukan ‘yan fashin daji da suka addabin yankin arewa maso yamma.

A cewar mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan, SP Gambo Isah, yaron mai shekara 14 ya amsa laifin kashe mutum biyu yayin wani hari da suka taɓa kai wa.

Gambo Isah ya ce yaron yana cikin waɗanda suka kai hari a Mallamawa cikin Ƙaramar Hukumar Jibia da kuma wasu a wajen Jihar Katsina, inda ya ce ya tuna lokacin da ya kashe mutum biyu.

Ya ce yaron ya kuma ya shiga hare-haren da aka kai a Dankulumbo da Kukar Babangida, duka a yankin Jibiya, sannan ya yi ƙwacen shanu da ba za a tantance adadin su ba.

Ba kasafai ake kama yara ƙanana ba da zargin taimaka wa ‘yan fashin duk da cewa ‘yan sanda sun sha kama mata da kayayyaki a kan hanyarsu ta kai wa miyagun.

Har yanzu wasu sassa na jihohin Kaduna da Zamfara da Katsina da Neja inda ‘yan fashin suka fi addaba da kashe-kashe da satar mutane na cikin ɗaukewar layukan sadarwa, matakin da gwamnatoci suka ɗauka da zummar daƙile ayyukan maharan.