Home Labaru Siyasa Magoya Bayan Tinubu Sun Yi Taron Rantsar Da Shugabannin Jihohi

Magoya Bayan Tinubu Sun Yi Taron Rantsar Da Shugabannin Jihohi

15
0

Kungiyar magoya bayan jigo a jam’iyyar APC Bola Tinubu, ya tsaya takarar shugaban kasa (TSG) ta gudanar da taron kaddamar da shugabannin ta na jihohi.

Taron da ya gudana a sakatariyar kungiyar ta kasa da ke nan Abuja a Asabar din nan ya baje kolin ayyukan Tinubu tare da rantsar da shugabannin kungiyar na jihohin Najeriya 36.

Tinubu wanda tsohon gwamnan jihar Legas ne yana da muradin  tsayawa takarar shugaban kasa domin maye gurbin Shugaba Buhari a  babban zaben 2023.

Kungiyoyi magoya bayan Bola Ahmad Tinubu daga sassan Najeriya daban-daban ne su ka yi dandazo a wajen taron.

Taron na zuwa ne mako biyu bayan dawowar jagoran na APC na kasa daga kasar Birtaniya inda ya shafe watanni yana jinya bayan an yi masa aiki.