Home Labaru Jiragen Yakin Najeriya Sun Yi Wa Mayakan ISWAP Ruwan Wuta

Jiragen Yakin Najeriya Sun Yi Wa Mayakan ISWAP Ruwan Wuta

47
0

Rundunar sojin saman Najeriya tace Jiragen yaƙin ta uku sun yi wa gwamman mayaƙan ƙungiyar (ISWAP) ruwan wuta a yankin arewa maso gabas.

Wata sanarwa da kakakin rundunar, Edward Gabkwet, ya fitar ranar Juma’a ta ce an kai hare-haren ne kan mayaƙan lokacin da suke taruwa a jiragen ruwa da zummar yin wata ganawa a Tumbun da ke kusa da Tafkin Chadi.

Rundunar ta ce bayan samun bayanan sirri ranar 20 ga watan Oktoba cewa jiragen ruwa kusan 20 na ‘yan ta’addan Boko Haram ko ISWAP na taruwa don ganawa a Tsibirin Tumbuns da ke Malam Fatori, jirage uku na rundunar Operation Hadin Kai suka shirya kai musu hare-hare ta sama.

Gabkwet yace Mummunan harin ya sa mayaƙan  da kowane jirgi ke ɗauke da mutum biyar zuwa shida sun fantsama neman tsira.