Home Labaru ‘Yan Nijeriya Uku Sun Lashe Gasar Karatun Kur’ani A Kasar Saudiyya

‘Yan Nijeriya Uku Sun Lashe Gasar Karatun Kur’ani A Kasar Saudiyya

879
0
‘Yan Nijeriya Uku Sun Lashe Gasar Karatun Kur’ani A Kasar Saudiyya
‘Yan Nijeriya Uku Sun Lashe Gasar Karatun Kur’ani A Kasar Saudiyya

Wasu ‘yan Najeriya su uku sun yi nasarar lashe manyan kyautuka a musabakar karatun Al-Kur’ani mai girma a matakai daba-daban da ta gudana a kasar Saudiyya.

Gwamnan Makka Khalid Al Faisal ya mika kyaututukan ga ‘yan Nijeriyan wanda suka hada da Idris Abubakar Muhammad da Amir Yunus Goro da kuma Abdulganiyyi Amin.

Gwani Idris Abubakar Muhammad wanda ya fito daga jihar Borno, ya zo na daya ne a ajin farko na izihi sittin ba tare da tafsiri ba, wanda hakan ya sa aka bashi kyautar riyal dubu 120 kimanin naira milyan 12 kudaden Nijeriya.

Amir Yunus kuwa,  ya zo na uku ne a ajin farko na izu sittin da tafsiri, inda ya samu kyautar riyal dubu 150 kimanin sama da Naira miliyan 14, yayin da Abdulganiyyu Amin ya zo na uku a aji na biyu a izu sittin ba tare da tafsiri ba, shima ya samu kyautar riyal dubu 40  kimanin naira miliyan 4 kenan.

Wannan dai ita ce musabakar karatun Al-Kur’ani ta sarki Abdulaziz karo na 41, wadda aka saba gudanarwa a kasar Saudiyya duk shekara.

Leave a Reply